Laraba 8 Yuli 2026 - 09:02
Shaidar Ayatullah Al-Uzma Jawadi Amuli Ga Shahidin Jagora + Bidiyo

Hauza/ Ayatullah Jawadi Amuli, yayin da yake jagorantar sallar jana’izar Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, ya bayyana taƙaitaccen bayani kan wasu kebantattun siffofi na Shahidin Jagoran a ƙarshen sallar, cikin wani nau’i na shaidar yabo da za ta kasance abin tunawa a tarihin duniya har abada.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an gudanar da sallar jana’izar Shahidin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da kuma shahidan iyalansa, da safiyar ranar Talata 16 ga Tir 1405 (7 ga Yuli 2026), a Masallaci Mai Tsarki na Jamkaran, inda Ayatullah Jawadi Amuli ya jagoranci sallar tare da halartar miliyoyin masu ƙaunar Shahidin.

A lokacin sallar, tsananin baƙin ciki ya bayyana a fuskar Ayatullah Jawadi Amuli, inda muryarsa ta cika da kuka, idanunsa suka zubar da hawaye saboda rashin wannan jagora mai gwagwarmayar al’umma.

Shaidar Ayatullah Jawadi Amoli ga Jagoran Al’umma

Ayatullah Jawadi Amuli yayin jagorantar sallar jana’iza ya bayyana manyan siffofi na musamman na Jagoran Shahidi cikin kalmomin shaida da addu’a, waɗanda za su kasance abin tunawa a tarihi:

اللَّهُمَّ إِنَّ هذَا الْمُسَجَّى قُدّامَنَا، عَبْدُکَ وَ ابْنُ عَبْدِکَ وَ ابْنُ أَمَتِکَ

Ya Allah! Wannan wanda aka shimfiɗa a gabanmu, bawanka ne, ɗan bawanka ne, kuma ɗan baiwarka ne.

نَزَلَ، نَزَلَ، نَزَلَ بِعِزِّ جَلَالِکَ وَ جَبَرُوتِکَ وَ عَظَمَتِکَ وَ مَلَکُوتِکَ

Ya sauka, ya sauka, ya sauka zuwa ga ɗaukakar zatinka, girman ka, ikonka, girmanka da mulkinka.

نَزَلَ بِعِزِّ جَلَالِکَ وَ جَبَرُوتِکَ وَ مَلَکُوتِکَ

Ya sauka zuwa ga girmanka, ɗaukakarka, ikonka da mulkinka.

اللَّهُمَّ إِنَّهُ نَزَلَ مُجاهِداً، مُبالِغاً، وَرِعاً، مُوَحِّداً، مُتَأَلِّهاً

Ya Allah! Lallai ya zo gare Ka yana matsayin mai jihadi, mai ƙoƙari matuƙa, mai tsoron Allah, mai tauhidi kuma mai zurfin sanin Allah.

اللَّهُمَّ، اللَّهُمَّ، اللَّهُمَّ، إِنَّهُ نَزَلَ عِنْدَکَ شَهِیداً لِلْإِسْلَامِ وَ الْقُرْآنِ وَالْعِتْرَةِ؛ هذَا أَوَّلاً

Ya Allah, Ya Allah, Ya Allah! Lallai ya zo gare Ka a matsayin shahidin Musulunci, Alƙur’ani da Ahlul Baiti. Wannan ita ce shaidarmu ta farko.

اللَّهُمَّ، اللَّهُمَّ، اللَّهُمَّ، إِنَّهُ نَزَلَ عِنْدَکَ قَتِیلاً لِلْإِسْلَامِ؛ قَتِیلاً لِلْأُمَّةِ الْمُسْلِمَة؛ قَتِیلاً لِسِیَاسِتِهَا؛ قَتِیلاً لِصِیَانَتِهَا؛ قَتِیلاً لِکِیَانِهَا؛ قَتِیلاً لِعَظَمَتِهَا وَ سِیَادَتِهَا وَ مَوْلَوِیَّتِهَا وَ وَحْدَتِهَا

Ya Allah, Ya Allah, Ya Allah! Lallai ya zo gare Ka a matsayin wanda aka kashe a tafarkin Musulunci; wanda aka kashe saboda al’ummar Musulmi; wanda aka kashe wajen kare manufofin Musulunci; wanda aka kashe domin kiyaye ta; wanda aka kashe domin kare ginuwar al’umma; wanda aka kashe domin ɗaukaka, shugabanci, wilaya da haɗin kan al’ummar Musulmi.

یَا مَنْ یَقْبَلُ الْیَسِیرَ وَ یَقْبَلُ الْیَسِیرَ، اقْبَلْ مِنْهُ وَ مِنَّا الْیَسِیرَ، إِنَّکَ عَلَی کُلِّ شَیْءٍ قَدِیرٌ

Ya Wanda kake karɓar aiki kaɗan kuma kake ba shi lada, Ka karɓi wannan ɗan aikin daga gare shi da kuma daga gare mu. Lallai Kai Mai iko ne a kan komai.

اللَّهُمَّ إِنَّهُ نَزَلَ بِعِزِّ غُفْرَانِکَ، وَ هُوَ عَبْدُکَ وَ مُحْتَاجٌ إِلَی رَحْمَتِکَ

Ya Allah! Lallai ya zo cikin kariyar girman gafararka, shi bawanka ne kuma yana buƙatar rahamarka.

اللَّهُمَّ احْشُرْهُ مَعَ الْأَئِمَّةِ الْهُدَاةِ الْمَهْدِیِّینَ

Ya Allah! Ka hada shi tare da Imamai masu shiryarwa waɗanda aka shiryar.

وَاخْلُفْ عَلَی أَهْلِهِ فِی الْغَابِرِینَ، صَلِّ عَلَیْهِ وَ عَلَیْهِمْ أَجْمَعِینَ، وَاحْشُرْنَا مَعَهُ مَعَ عِنَایَتِکَ وَ عِنَایَة مُحَمَّدٍ وَ عِتْرَتِهِ الطَّاهِرِینَ

Ka maye masa gurbin alheri ga iyalansa da suka rage, Ka yi masa da su baki ɗaya salati da rahama, kuma Ka tara mu tare da shi ta hanyar kulawarka da kulawar Annabi Muhammad (SAWA) da tsarkakakkun zuriyarsa.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha